Laraba 17 Yuni 2026 - 14:03
An Fara Zaman Juyayin Ashura na Goman Farko na Watan Muharram a Garin Doma ta Jihar Nasarawa / Jaddada Muhimmancin Yin Koyi da Makarantar Karbala Wajen Yaki da Zalunci + Hotuna

Hauza/ A yayin shiga sabuwar shekarar Musulunci ta Hijra 1448 da kuma ranar farko ta watan Muharramul Haram, an kaddamar da zaman juyayi da makokin shugaban shahidai, Hazrat Aba Abdillahil Husain (AS), tare da halartar mabiya da almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) a garin Doma dake jihar Nasarawa a kasar Nijeriya.

A cewar rahoton Kamfanin Dillacin Labaran Hauza, wannan taro wanda ke gudana tare da takwarorinsa a fadin Nijeriya da sauran sassan duniya, an shirya shi ne a harabar babban masallacin juma'a na garin Doma, da nufin girmama alamomin addini da taya Manzon Allah (SAWA) da iyalan gidansa tsarkaka (AS) jajen kisan gillar da dakarun Yazidu dan Mu'awiya suka yi wa Imam Husaini (AS) da sahabbansa a shekara ta 61 bayan Hijra.

A ranar farko ta wannan taro, "Malam Muhammad Dahir Usman", wakilin almajiran Sayyid Zakzaky na garin Doma, ya gabatar da jawabi ga mahalarta. Ya fara jawabinsa ne da jaddada muhimmancin sani da bai wa kididdigar kalandar Musulunci muhimmanci fiye da kalandar Miladiyya, inda ya bayyana ta a matsayin tushen gudanar da ibadu da alamomin addini na Musulmi.

Malam Dahir Usman ya ci gaba da bayani kan daukaka da matsayi na musamman na Hazrat Sayyidush Shuhada (AS) a duniyar Musulunci, inda ya kara da cewa: "Duk da cewa Imam Husaini (AS) shi ne mafi daraja da daukaka a cikin dukkan halittu a zamaninsa, bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen sadaukar da ransa, dukiyarsa, da iyalansa domin ceton addinin Musulunci da raya shi."

Haka kuma, ya yi kira ga Musulmai da su kasance masu juriya da jaruntaka, tare da jaddada cewa barazana ko tsoron mutuwa da makiya ke yi kada su taba katange muminai daga tafiya a kan tafarkin gaskiya.

Wakilin na 'yan uwa a garin Doma ya karkare jawabinsa da bayyana Ashura a matsayin wata babbar makaranta kuma madubin koyi wajen yakar zalunci da azzalumai. Ya kawo misali da ci gaba da ɗaukakar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda ya ce: "Kasar Iran ta zama babbar kasa mai fada a ji (Super Power) a duniya ne sakamakon riko da addinin Musulunci na gaskiya, makarantar Imam Husaini (AS), da tafarkin Ahlul Bait (AS)."

Ana tunatar da cewa, wannan taro na samun ilimi da raya juyayi zai ci gaba da gudana har tsawon darare 10 zuwa ranar Ashura a garin na Doma.

An Fara Zaman Juyayin Ashura na Goman Farko na Watan Muharram a Garin Doma ta Jihar Nasarawa / Jaddada Muhimmancin Yin Koyi da Makarantar Karbala Wajen Yaki da Zalunci

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha